8 Satumba 2020 - 11:57
Beirut: Fada Ta Barke Tsakanin Magoya Bayan ‘Yan Siyasa

Fada da makamai ta barke tsakanin magoya bayan jam’iyyar Mustagbal ta Sa’adul Hariri tsohon firai ministan kasar ta Lebanon da kuma masu goyon bayan yayansa Baha’ul Hariri a kan titin –Sabon Titi- na birnin Beirut a jiya da yamma.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon, ta bayyana cewa an kawo karshen fadan ne bayan da sojoji suka shiga tsakani, amma an rasa ran mutum guda.

Kafin haka dai Baha’ul - hariri ya sha fitowa cikin masu zanga-zangar na kin siyasar kaninsa Sa’adul Hariri, wadanda suka hada da ta cin hanci da rashawa da kuma nuna adawarsa da yadda Sa’adu yake daukar makaman kungiyar Hizbullah ta kasar.

342/